ADDU’A ITA CE IBADA 1-11

ADDU’A ITA CE IBADA 01

Addu’a Ibada ce mai zaman kanta, wanda a ke so musulmi ya yawaita yinta domin ita ce mai tabbatar da alaƙa tsakanin Allah da bawan Sa. Manzon Rahama ya ce: “Addu’a ita ce Ibada”.

A aya ta 60 a suratul Ghafir kuma Allah Madaukakin Sarki Ya ce:

وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ ۚ

Kuma Ubangijinku ya ce: “Ku roƙe ni in amsa muku.”

Addu’a da mu ke gani babu wani maganin da ya kai ta warkar da duk wata fitinar duniya da lahira, mu yi ta addu’a domin ita ce mai kawar da wasu bala’in gaba ɗaya kuma mai rage ƙarfin ƙaddarar da babu makawa sai ya same mu.

A suratul baqara Allah mai girma da buwaya ya ce:

((وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ ۖ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ ۖ فَلْيَسْتَجِيبُوا لِي وَلْيُؤْمِنُوا بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ.))

“Kuma idan bãyi Na suka tambaye ka game da Ni, to, lalle Ni Makusanci ne (wato yana kusa). Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓaTa. kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.”

Manzon Allah (SAW) ya ce : “Idan ɗayanku zai yi addu’a ka da ya ce Allah ka amsa min in ka ga dama kawai ya nace wajen roƙo kuma ya sa ran an karɓi addu’ar. Domin Allah ba ya jin nauyin bada ko wane irin abu ne da ya bayar dashi”.

ADDU’A ITA CE IBADA 02

Sannan ana son bawa ya rinƙa lura da lokuta da yanayin amsa addu’a:

  1. Kamar ƙarshen dare na ko wane rana.
  2. Tsakanin kiran Sallah da Iƙama.
  3. Sai ranar Jumu’a tsakanin la’asar da Magriba.
  4. Addu’ar iyaye ga ƴaƴansu.
  5. Lokacin da mutum ke halin tafiya.
  6. Lokacin da mutum ya ke cikin tsanani ko mawuyacin hali.
  7. Idan bawa ya yi sujjada.
  8. Haka nan in mutum yana azumi lokacin shan ruwa dss.

Sake da addu’a kuskure ne babba ga ɗan adam, duk wani hali na tsanani da bawa ya tsinci kansa to ya jajirce da addu’a, yana nan Allah zai amsa masa kuma Ya fitar da shi cikin halin jarabawar sa mutuƙar bai yi gaggawa ba. Yin addu’a yana nuna kwaɗayin bawa wurin neman samun rahamarsa.

Nabiyut Rahama ya ce: “Ka da mu daina addu’a domin ita ce mai tabbatar da alaƙar mu da Allah.”

Kuma ya ce “Mafi rowar cikin mutane shi ne mai yin rowar sallama, kuma mafi gajiyawar mutane shi ne ya ke kasa yin addu’a”.

Manzon Allah (SAW) ya sake cewa: “Babu wani abu mai karamci a wurin Allah (SWT) sama da addu’a”.

ADDU’A ITA CE IBADA 03

Ana son mai addu’a ya kula da waɗannan duk lokacin da zai yi addu’a:

1.Ya roƙi Allah shi kaɗai ka da ya haɗa shi da wani abokin tarayya domin wannan yana warware musuluncin mutum, ka da ka haɗa Shi da wani wurin bauta in zaka roƙe shi to ka aika roƙon gare Shi kai tsaye amma ka da ka aika ɗan sako ko sanya labule.

Kamar mutum ya ce Yaa Shehu ka amsa mun addu’a na ko wani waliyyi, wato shi za ka roƙa wata buƙata shi kuma sai ya roƙa maka Allah har ma kana jin idan baka yi tawassuli da shi ba addu’ar ba za ta amsu ba wannan shirka ce ya jama’a.

In mutum na yin haka to ya gyara domin ka da addu’arsa ta zama kamar an jefa dutse cikin ruwa, Shi Allah Ya fi so ka roƙe shi da kanka, kuma ba ya gajiya da amsa roƙon bawa. Ba kamar mutum bane da kullum in kana roƙon sa sai ya ji haushin ka ya gaji da kai to shi kana rokon Sa ne yana ƙara sonka.

2.Nisantan cin haramun da rayuwa cikinta, da nisantan manyan zunubai da za su sanya Allah fushi da bawa. Kamar yanda haramun take ɓata dukiyar bawa haka ma tana taɓa duk abun da ya shafe shi har da addu’ar sa. Kuma munanan dabi’u da manyan laifuka suna iya kawo tsaiko wurin amsan addu’a tun da Allah na fushi da bawan.

ADDU’A ITA CE IBADA 04

3.Tsayar da zuciya da nutsuwa, shi yasa a ke son ibadan da dare domin babu hayaniya ko abubuwan ɗauke hankali. Ya zama zuciyar ka tana halarce kuma kana sanin me kake faɗi kake roƙo. Domin Allah (SWT) Ya ce: “Ni ina dai-dai in da bawana ya ke zato na kuma ina tare da shi in Ya roƙe Ni”.

Ka da ka yi addu’a har ka gama amma baka san ma me ka faɗi ba hankalin ka na wasu tunanin abu can daban, to ba a san mai addua ya kasance haka. Ka tattaro dukkanin hankali da tunanin ka ka sanya a cikinsa.

4.Roƙon Allah da kuma yaƙinin za a amsa da sanyawa a rai cewa wannan addu’ar tabbas za a amsa, da jin cewa Allah Yana ganin ka kuma Yana sauraron ka.

Da gujewa mummunan addu’a ga wani, haka nan mutum ya yi muguwar addu’a na wani ya lalace ko na yanke zumunta. To ba a amsan irin wannan adduar.

ADDUA ITA CE IBADA 05

5. Kuma ana son mutum ya rinƙa haɗe addu’a a cikin jimloli kaɗan da kiyaye wuce gona da iri, ya zama kuma addu’ar da hikima a cikinta. Ka da ka rinƙa cewa Allah Ka bani abincin da zan ci, shinkafa ƴar gwamnati ta kamfanin ɗan gote, kuma ka bani wake manya na sawa a abinci da qanana na yin ƙosai, haka nan Allah da mai da kayan miya da nama. Ka ga wannan dogon labari ne kuma babu hikima ko girmamawa a cikin addu’ar. Sannan ka da ka rinƙa faɗi ko iyakance abubuwan da ke cikinta domin ni’imomin Allah tana da yalwa. Ka ce Allah ka azurta ni da abinci mai kyau da zan ci ni da iyalaina ka kare mu daga yunwa, kuma ka azurta mu da tufafi ka kare mu daga talauci. Domin Allah Sarkin masu hikima da basira ne duk abun da ka faɗi ya sani kuma Ya fahimce ka Zai kuma baka wanda ya fi tunaninka.

Nana Aisha (RA) ta ce: Manzon Allah (SAW) ya shigo in da nake alhalin ina addu’a (shi kuma akwai abun da ya ke nema a gurina sai ban je gurinsa da wuri ba) Sai ya ce : “Ya Aisha ki dinga tattare addu’a da wasu ƴan jumloli masu mamayewa”. Yayin da na gama sai na ce ya Manzon Allah (SAW) waɗanne ne jumloli masu mamaye komai?

Sai ya ce : “Ki ce: Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alkhairi na duniya da na lahira wanda na sani da wanda ma ban sani ba. Kuma ina roƙon Ka aljannah da duk wani aiki da zai kusantar da ni izuwa gareta. Kuma ina neman Ka tsare ni daga wuta da duk wani aiki da zai kusantar dani zuwa gareta. Kuma ina roƙon ka duk wani abu da Annabi Muhammad (SAW) ya roƙe Ka. Kuma ina neman tsarin ka da duk abin da Annabi Muhammad (SAW) ya nemi tsarinsa a gare ka. Kuma duk abin da Ka zartar a kaina ka sanya ƙarshen sa ya zama alkhairi a gare ni”.

Kun ga waɗannan ƴan kalmomi ne da zaka faɗi cikin ƴan mintuna masu ɗauke da komai da ɗan adam ya ke nema ko zai buƙata.

ADDU’A ITA CE IBADA 06

Haka nan mu koyon yin addu’a ga wanin mu yana da falala da alkhairai, wato ka rinƙa sanya mutane a cikin addu’oin ka da ka zama mai son kai kamar yanda Annabi (SAW) ya ke yi:

Safwan bn Abdullahi bn Safwan Ya kasance yana auren Dardaa’u ƴar Abi Dardaa’u, ya ce na zo wajensu daga sham sai na sami ummu Darda’i a gida ban sami Abi Darda’i ba. Sai ta ce ka yi niyyar hajji bana ne? Sai na ce Eh. Sai ta ce to ka yi mana addu’ar alkhairi saboda Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cewa: “Lallai addu’ar mutum musulmi karɓaɓɓiya ce in ya yi wa ɗan’uwan sa alhali ɗan’uwan ba ya nan. Allah zai sanya wani mala’ika a dai-dai kansa duk sanda ya yi wa ɗan’uwan sa addu’ar alkhairi sai mala’ikan ya ce: Ameen Allah Ya amsa kuma Ya baka kwatan-kwacin abin da ka roƙar masa”.

Ya ce sai na gamu da Abu Darda’i a kasuwa sai ya faɗa min irin abin da ta fada min shima ya jiyo daga Manzon Allah (SAW)”.

Haka nan Sayyidna Abubakar (RA) ya ce “Tabbas yi wa ɗan’uwa addu’a ba tare da ya sani ba kuma saboda Allah a ka yi addu’ar to Allah na karɓar wannan addu’ar”. Saheeh.

Thabit ya ce Anas (RA) ya kasance idan zai yiwa ɗan’uwan sa musulmi addu’a yana cewa: “Allah ka sanya shi cikin addu’o’in bayin ka masu biyayya waɗanda su ba azzalumai ba ne ba kuma fajirai ba ne, waɗanda su ke tashi sallar dare sannan su ke yin azumi da rana”. Saheeh. Kun ga wannan addu’a ce mai tattare da alkhairi da mutum zai yi ma ɗan’uwan sa.” Saheeh

Anas (RA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya kasance yana shigowa gidan mu sai ya shigo wata rana sai ya yi mana addu’a sai Ummu Sulaim ta ce ga wannan ɗan ƙaramin mai yi maka hidima ba za kai masa addu’a ba?

Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Ubangiji Ka yawaita arziƙinsa da ƴaƴansa, kuma Ka tsawaita rayuwar sa kuma Ka gafarta masa”. Sai ya yi min addu’a bisa abubuwa guda uku ya ce sai da ta kai na binne tsakanin jikoki da ƴaƴa ɗari da uku, kuma gonata sau biyu take fitar da iri a ci a shekara, kuma rayuwata ta yi har zamto ina jin kunyar mutane sannan ina fatan rahamar Ubangiji.” Saheeh.

ADDU’A ITA CE IBADA 07

Haka nan ana son bawa idan ya yi ma kansa addu’a to ya yi ma sauran mutane ko in zai yi a cikin mutane to ya yi jama’u ka da ya zama mai rowa musamman in yana cikin jama’a ne.

Abdullahi bn Amr (RA) ya ce wani mutum ya ce: “Ya Allah Ka gafarta mini da kuma Annabi (SAW) mu kaɗai”. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce : “Tabbas ko ka katange gafarar Allah game da mutane masu yawa”. Saheeh.

Haka nan ana son bawa ya guji yin muguwar addu’a domin Manzon Rahama ba ya haka:

‘Dufail ɗan Amru Addausy ya zo wajen Manzon Allah (SAW) sai ya ce ya Manzon Allah (SAW) tabbas ƙabilar Daus ta yi saɓo kuma ta ƙaryata addini ka yi mata mummunar addu’a. Sai Manzon Allah (SAW) ya fuskanci alƙibla ya kuma ɗaga hannunsa sama kowa ya yi tunanin Annabi (SAW) zai musu mummunar addu’a kawai sai ya ce : “Ya Ubangiji! Ka shiryar da ƙabilar Daus kuma Ka sa su zo su na masu miƙa wuya”. Saheeh.

Nana Aisha (RA) ta ce ta ga Annabi (SAW) yana addu’a a lokacin kuma ya dɗaga hannayen sa sama yana cewa: “Tabbas ni mutum ne ka da ka yi min uƙuba ko wane ɗaya cikin muminan da na cutar da shi ko na aibata shi ka da Kai min uƙuba a kansa”.

Kun ga a nan mun koyi cewa Annabi (SAW) yana ɗaga hannunsa in zai yi addu’a, kuma yana fuskantar alƙibla. Kuma ba ya yin muguwar addu’a ga mutane, yana kuma yawaita addu’ar shiriya da alkhairi.

Duk abun da ka ke so ka roƙi Allah kamar yanda muka karanta babu abun da Annabi ba ya roƙon Allah, kamar neman tsari daga azabar kabari, daga mummunanr makoci, talauci, daga mummunan tsufa, zalunci, daga alfasha, kasala, bashi mai nauyi, daga mummunan ƙarshe kai daga komai ma don haka sai muma mu roƙi komai.

ADDU’A ITA CE IBADA 08

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ana amsa addu’ar ɗayanku matuƙar bai yi addu’ar saɓo ba ko ta yanke zumunci, ko ya yi gaggawa har ya rinƙa cewa na roƙa anƙi a amsa min kawai sai ya daina yin addu’ar”. Saheeh.

Domin Shi Allah Ya na son mai addu’a mai naci, Manzon Allah (SAW) ya ce : “Idan ɗayan ku zai yi addu’a to ya nace wajen addu’ar sannan ka da ya ce Ya Allah in Ka ga dama Ka bani abin domin shi Allah babu wanda ya isa ya tilasta masa”.

SHAIKHUL ISLAM IBNU TAIMIYYA yana cewa: Ya kamata mutane in za su yi addu’a to su yi addu’a wanda shari’a ta karantar, Addu’ar da ayoyin Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW) suka kawo. Domin babu shakka duk wata addu’a da ta zo a cikin littafin Allah da sunnar Manzon Allah (SAW) to wannan addu’a ba a shakkar falalarta ko kuma kyaunta.”

Ya cigaba da cewa: Riƙo da addu’oin Annabi Muhammad shi ne tafarki Madaidaici luma shi ne tafarkin mutanen da Allah Maɗaukaki ya yi musu ni’ima.”

Haka nan mu zama masu ƙoƙarin koyo addu’oin Manzon Allah da kuma haddace su musamman na safiya da maraice da kwanciya, da ƙanana na al’amuran rayuwa waɗanda za su baka kariya in kuma ka mutu ne ka yi da safe kana cikin waɗanda ake ma fatan samun rahama haka da maraice kafin wayewar gari. Kuma mu koyar da ƴaƴan mu su girma da shi.

Tsarki ya tabbatar gare K Ya Allah, tare da gode maka, na tabbata babu abin bautawa bisa da cancanta sai Kai kaɗai, muna neman gafarar Ka, kuma muna tuba zuwa gare Ka,Ya Allah muna roƙon Ka karɓi addu’oin mu domin Kai kaɗai ne mai karɓar ayyuka, kuma Kai mai iko ne a dukkan komai, Ya Allah muna roƙon Ka gafarta mana zunuban mu ka zaunar da kasar mu lafiya.

ADDU’A ITA CE IBADA 09

Kamar yanda na faɗa koyon adduo’in da Manzon Allah (SAW) Yake yi suna da falala sosai, zan kawo wasu daga cikon adduo’in domin mu rinƙa yi.

((ﻋﻦ ﻫﺸﺎﻡ ﺑﻦ ﻋﺮﻭﺓ، ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ، ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ اﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ: ﺃﻥ اﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ اﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ:

Daga A’isha (RA) cewa: Lallai Annabi (SAW) ya kasance ya na cewa:

((اﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ اﻟﻜﺴﻞ ﻭاﻟﻬﺮﻡ، ﻭاﻟﻤﺄﺛﻢ ﻭاﻟﻤﻐﺮﻡ، ﻭﻣﻦ ﻓﺘﻨﺔ اﻟﻘﺒﺮ، ﻭﻋﺬاﺏ اﻟﻘﺒﺮ، ﻭﻣﻦ ﻓﺘﻨﺔ اﻟﻨﺎﺭ ﻭﻋﺬاﺏ اﻟﻨﺎﺭ، ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻓﺘﻨﺔ اﻟﻐﻨﻰ، ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﻓﺘﻨﺔ اﻟﻔﻘﺮ، ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﻓﺘﻨﺔ اﻟﻤﺴﻴﺢ اﻟﺪﺟﺎﻝ، اﻟﻠﻬﻢ اﻏﺴﻞ ﻋﻨﻲ ﺧﻄﺎﻳﺎﻱ ﺑﻤﺎء اﻟﺜﻠﺞ ﻭاﻟﺒﺮﺩ، ﻭﻧﻖ ﻗﻠﺒﻲ ﻣﻦ اﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻛﻤﺎ ﻧﻘﻴﺖ اﻟﺜﻮﺏ اﻷﺑﻴﺾ ﻣﻦ اﻟﺪﻧﺲ، ﻭﺑﺎﻋﺪ ﺑﻴﻨﻲ ﻭﺑﻴﻦ ﺧﻄﺎﻳﺎﻱ ﻛﻤﺎ ﺑﺎﻋﺪﺕ ﺑﻴﻦ اﻟﻤﺸﺮﻕ ﻭاﻟﻤﻐﺮﺏ)). [رواه البخاري ومسلم].

Allahumma inni auzu bika minal kasali wal harami, wal ma’athami wal magram, wa min fitnatul qabri, wa azhabil qabri, wa min fitnatin nari wa azabin nari, wa min sharri fitnatul gina, wa’auzhu bika min fitnatul faqri, wa’auzu bika min fitnatul masihi dajjal, Allahumagsil anni khadayaya bi maa’i thalji wal barad, wa naq qalbi minal khadayaya kamaa naqaitu thaubul abyadu munad danas, wa ba’id baina khadaayaya kama ba’atta bainal mashriqi wal magrib.

Ya Allah! Ina neman tsarin Ka daga kasala (lalaci) da tsufa, da laifuka da fitinar bashi, kuma ina neman tsarin Ka daga fitinan ƙabari da azaban ƙabari da fitinar wuta da azabar wuta, da fitinar wadata. Kuma ina neman tsarin Ka daga fitinar talauci ina neman tsarin Ka daga fitinar Masihu Dajjal. Ya Allah! Ka wanke laifukana da ruwa da ƙanƙara da sanyi, Ka tsarkake zuciya ta daga laifuka kamar yanda Ka tsarkake farin tufafi daga ƙazanta. Ka nesanta tsakani na da laifuka kamar yanda Ka nesanta tsakanin gabas da yamma.”

Allah Ya bamu ikon yin wannan addua.

ADDU’A ITA CE IBADA 10

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ‏:‏ كَانَ مِنْ دُعَاءِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم‏:‏

An karbo daga Abi Huraira (RA) ya ce yana daga cikin addu’o’in Manzon Allah (SAW) cewa:

((اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ جَارِ السُّوءِ فِي دَارِ الْمُقَامِ، فَإِنَّ جَارَ الدُّنْيَا يَتَحَوَّل))ُ‏.‏

Allahumma inni Auzu bika min jaril su’i fiy daaril muqami, fa inna jarad-dunya yatahawwalu.

Ya Allah ina neman tsarin Ka daga mummunan maƙoci a gidan dawwama/zama (Lahira) domin maƙocin duniya yana iya canja gida. [Adabul Mufrad].

Annabi Muhammad (SAW) ya kasance yana karanta wannan addu’a:

((ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﻣﻨﻜﺮﺍﺕ
ﺍﻷﺧﻼﻕ، ﻭﺍﻷﻋﻤﺎﻝ، ﻭﺍﻷﻫﻮﺍﺀ”.)) [ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ].

Allahumma inni auzu bika min munkaratil akhlaqi, wal a’amali, wal ahwa’.

Yaa Allah! Ina neman tsarin Ka game da sharrin munanan halayya, da munanan ayyuka, da kuma son zuciya.

ADDU’A ITA CE IBADA 11

Daga Anas (RA) ya ce: “Mafi yawan addu’ar Manzon Allah (SAW) ita ce:

((اللهم ربنا آتنا في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة وقنا عذاب النار.))

Allahumma Rabbana Aatina, fid-dunya, hasanah, wa fil akhirati hasanah, wa qinaa azaban naar.

“Yaa Ubangiji! Ka bamu kyakykywa a duniya da kuma lahira, kuma ka karemu/kiyayemu daga azabar wuta.
Annabi yana yawaita fadin wannan addu’a wacce ta kunshi alkhairan duniya da lahira.

Yana da kyau mu yi riko da addu’oin Annabi Muhammad (SAW) uk mutumin da ya ke son Manzon Allah (SAW) to ya kamata ya binciko addu’oin sa ya yi riko da su. Allah Ya amsa mana addu’oin mu.

🖎Ƴar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar.

Ba a yarda a canza komai na cikin rubutun nan ba, ba a yarda a dauka a buga shi a cikin takarda ko littafi ba tare da izinin mai haqqin rubutun ba. Kuma ba a yarda a sanya shi a wani wuri da babu tarbiyyan musulunci ba. Allah Yana kallon ka/ki da fatan za a ji tsoron Sa a kiyaye.

Ga mai buqatar turo mun da saqo zai same ni a halima.lawal@aun.edu.ng